Hotunan takarar Gwamna Samuel sun mamaye garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe .
An yi rubutun wasu sakonni a jikin fastocin takarar Ortom da suke neman ya kai batun hana kiwo a fili majalisar dattijai.
Sai dai kuma Babban Sakataren yada labarai na Gwamnan, Terver Akase, ya ce hakan shine burin mutane kuma ba za su hana shi yiwuwa ba.
A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, an wayi gari an ga fastoci dauke da hoton gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a matsayin dan takarar sanata sun mamaye Makurdi, babban birnin jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ga fastocin da kungiyar Diversity Managers Group ta dauki nauyi a shataletalen gidan Gwamnati, Wurukum, North Bank da yankin Wadata da ke garin Makurdi.
Hotunan na dauke da rubutu daban-daban kamar su, “Muna goyon bayan Ortom don zama dan Majalisar Dattawa a 2023 “, “isar da dokar hana kiwo ga Majalisar Dattawa.”
Da yake martani a kan ci gaban, Babban Sakataren yada labarai na Gwamnan, Terver Akase, ya ce a takaice, “Burin mutane ne don haka gwamnan ba zai hana su ba.
Yana samun irin wannan fitowar da fatan alheri.”
Jaridar The Nation ma ta ruwaito Akase yana cewa: “Gwamna Ortom na da sauran shekaru biyu na jagorantar Benuwe kuma a nan ne inda ya maida hankali a yanzu.”
A wani labarin, Ofishin mataimakin shugaban ƙasa yace gasar neman tikitin takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 yana daɗa jan hankali, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Sai dai ofishin ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, bashi da niyyar yin takarar shugaban ƙasa a yanzu.
Kakakin mataimakin shugaban, Laolu Akande, shine ya faɗi haka a wani jawabi daya fitar yau a babban birnin tarayya Abuja.
Kafin hakan dai an sa ran mataimakin shugaban kasan farfesa yemi osinbanjo zai tsaya takarar shugabancin najeriya a zabe mai gabatowa.