A kasar Argentina mutane 12 suka gamu da ajalinsu bayan da suka sha gurbatacciyar hodar ibilis Koken (Cocaine) wasu 50 kuma na cikin wani hali a asibiti dake birnin Buenos Aires.
‘Yan sandan yankin ne suka kai samame inda suka rutsa mutane da ke da hannu wajen saida hodar ibilis din.
A cewar Jami’an tsaro har yanzu basu gano abinda aka gurbata hodar ibilis din da shi ba.
Jami’an sun gargadi mutanen da suka sayi hodar ibilis daga yankin dan tsakanin nan da kada su kurkura su yi amfani da ita.
A wani labarin na daban Argentina ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya duk da rashin nasara a wasansu da Brazil na jiya talata da suka tashi babu kwallo amma rashin nasarar Chile da Uruguay ya taimakawa mata.
Argentina ita ce kasa ta biyu a kudancin Amurka da ta samu gurbin bayan Brazil da ta samu nata gurbin a farkon makon jiya.
Samun tikitin na Argentina ya mayar da jumullar kasashen da zuwa yanzu yanzu suka samu tikitin na zuwa Qatar guda 13.
Yanzu haka dai kasashen turai 10 ciki har da Portugal da kuma Italiya zakarar Euro ne za su yi dakon wasannin cike gibi gabanin samun tikitin na Qatar.