Al’ummar Hausawan da mazauna garin Sagamu da ke jihar Ogun da dama ne suka fito suna gudanar da zanga-zangar lumana domin neman a yi adalci kan hukuncin zaben gwamnan Jihar Kano da ke gaban kotun koli.
‘Yan Arewa masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne da kananan yara, sun bi manyan titunan garin Sagamu, suna rera wakokin hadin kai tare da yin kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sa baki a lamarin don dakile zargin kulla makarkashiyar karya doka da oda a fadin Nijeriya.
‘Yan Arewa mazauna garin Sagamu dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban, sun bayyana fargabar cewa rikicin Kano na iya yaduwa zuwa Kudancin kasar nan idan har bangaren shari’a ya yi amfani da duk wata dabarar da za ta bi wajen tabbatar da sabanin abun da masu kada kuri’a a Jihar Kano suka zaba wanda aka bayyana a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a zaben gwamna a jihar.
Sun yi kira da a yi adalci da zai kawo zaman lafiya, sun kuma yi gargadin cewa zaman lafiya na iya karanci a Nijeriya idan ba a yi abun da ya dace kan lamarin shari’ar ta Kano ba.
Wasu daga cikin rubuce-rubucen da aka rubuta a allunansu an rubuta: “Ka guji zubar da jini, a tabbatar da zaman lafiya a Kano”; “Muna zaune a kudu lafiya, amma rashin adalci a Kano na iya yada tashin hankali”; “Matsalar Kano na iya yaduwa zuwa Kudu”; “A yi adalci don samun zaman lafiya a Kano” d
a sauransu.
Source: LEADERSHIPHAUSA