Mambobin harkar musulunci a najeriya sun gudanar da janazar daya da aka kashe daga cikin takwas, wadanda jami’an tsron najeriya suka kashe yayin da suke gabatar da gangamin lumana domin tunawa da ranar cika kwana arba’in da kisan Imam Hussin (S.a) da sojojin sarkii yazidu dan mu’awiya sukayi a shekara ta 61 bayan hijira.
Su dai mambobin na harkar msulunci a najeriya sukan fito domin nuna goyon baya ga jikan na manzon Allah (S) amma ma’aikata, jami’an tsaro kanyi dirar mikiya a kan wannan taro duk shekara idan ana gudanar dashi wanda kuma hakan kanyi sanadin rasa rayuka da jin raunuka a bangaren mambobin harkar musulunci a najeriyar.
Gidan talbijin na Press Tv yayi fira da jagoran harkar musulunci a najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, inda da akayi masa tambaya kan dalilin da yasa jami’an tsaron najeriyar kan dira kan mambobin na harkar musulunci a najeriya yace su kansa basu san dalili domin hatta masu kawo harin basu iya bada dalili kan wannan hare haren ta’addanci da suke kaiwa kan tarukan da almajiran malamin ke shiryawa ba.
A firar da gidan talbijin na press tv din dai yayi da sidi munir daya aga cikin almajiran sheikh zakzaky din ya bayyana cewa zuwa yanzu basu iya tantance mutane nawa suka rasa rayukan su sakamakon harin jami’an tsaron ba amma dai suna bibiya domin a kwai wadanda jami’an tsaron suka kwashe suka tafi dasu inada ba’a sani ba saboda haka dole sai an kammala bincike sannan za’a tabbatar amma dai zuwa yanzu an tabbatar da shahadar mutum daya wanda shine ae janazar sa yanzu hakan.
Abdullahi Muhammad Musa shima daya ne daga cikin mambobin harkar musulunci kuma ya bayyana takaicin kan yadda jami’an tsaron da ake saya ma makamai kuma abiya su albashi a baitul malin kasa domin su kare rayuwa da lafiyar ‘yan kasa a su karata da kisa gami da raunata ‘yan kasa, kuma a dai dai lokacin da suke da aikin daya kamata suyi a jihohin da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka addaba amma sun kasa zuwa can sun karata da kisan fafaren hula marasa makami kurum saboda suna aiwatar da addinin su yadda suka fuskanta kuma kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar aiwatarwa.