Hukumomi a Gaza sun ce kashi 70 cikin 100 na al’ummar yankin “an tilasta musu barin gidajensu” saboda hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai musu.
Kiyasi ya nuna cewa al’ummar Gaza sun kai mutum miliyan 2.3.
A wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar a ranar Talata ya ce, hare-haren Isra’ila sun lalata kashi 50 cikin 100 na gidajen da ke fadin Gaza, kuma kashi 10 cikin 100 na gidajen an lalata su baki daya ko kuma ba za a iya zama a cikinsu ba.
Kazalika sanarrwar ta ce rabin asibitoci da kashi 62 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza ba sa aiki.
0800 GMT — Israila za ta kwace ikon wanzar da tsaro a Gaza bayan yaki: Netanyahu
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa za ta “kwace ikon wanzar da tsaro” a Gaza har sai abin da hali ya yi idan ta kammala yaki da kungiyar Hamas.
“Isra’ila za ta dauki alhakin tabbatar da tsaro har sai abin da hali ya yi,” in ji shi a hirar da ya yi da kafar watsa labarai ta ABC News.
“Idan ba mu dauki nauyin tabbatar da tsaro ba, za mu fuskanci barkewar ta’addanci daga kungiyar Hamas irin wanda ba mu taba tsammani ba,” a cewarsa.
0730 GMT — Isra’ila ta rusa masallatai 56 a Gaza
Isra’ila ta lalata masallatai 192, cikin har da 56 da ta lalata baki daya tun da ta soma kai gari a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gaza a sanarwar da ya fitar Litinin da maraice.
“Hare-haren da Isra’ila take kai wa a Gaza sun lalata masallatai 192, ciki har da 56 da ta rusa baki daya, baya ga coci uku da ta rusa,” a cewar mai magana da yawun ofishin na Watsa Labarai Salama Marouf a taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Gaza.
Ya kara da cewa hare-haren sun rusa cibiyoyin kiwo lafiya 192 da kuma motocin daukar marasa lafiya 32 kana sun lalata cibiyoyin kiwon lafiya 113, yayin da asibitoci 16 da cibiyoyin samar da lafiya 32 suka daina aiki.
Source: TRThausa