Shugabannin Najeriya sun yi taro domin shawo kan matsalolin rashin tsaro, Gwamnan Delta yace babu ja-da-baya a kan batun hana kiwon dabbobi a hanyoyin Kudu.
Sarkin Musulmi da Gwamnoni sun fadi yadda matsalar tsaro za ta zama tarihi Fitattun shugabannin addinai da siyasa a Najeriya sun sake yin taro a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, 2021, a game da matsalar tsaro da ake fama da ita da kuma hanyoyin da za’a bi domin magance su.
Jaridar The Nation ta ce shugabannin sun yi kira ga gwamnati, ta tashi-tsaye, domin bin hanyoyin magance matsalar.
Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya ce babu ja da baya a kan matakin da gwamnonin jihohin Kudu suka dauka na haramta yawo da dabbobi a fili.
”Babu wanda ke bin mu bashin neman afuwa, saboda gaskiya muka fada, kuma muna ganin mun fadi gaskiyar ne domin cigaban kasar nan.” Inji Ifeanyi Okowa.
Mai girma gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu da Sultan, Alhaji Sa’ad Abubakar III sun bukaci a ba Sarakunan gargaji matsayi a cikin dokar kasa. Sultan Sa’ad III ya bukaci a cire shamakin binciken da dokar kasa ta ba wasu shugabanni, ya ce yin hakan zai sa wadannan shugabannin suyi abin da ya dace.
The Cable ta rahoto Sa’ad Abubakar III yana wanke sojoji daga zargin gaza magance matsala, ya ce nauyin da yake kan jami’an tsaron a yanzu ne ya yi masu yawa.
Ganin yadda ake fama da satar ‘yan makaranta, kungiyar ‘daliban Najeriya watau NANs, ta bada shawarar rufe makarantun da ke Arewa ta tsakiya da yamma.
A na ta bangaren, gwamnatin Birtaniya ta sha alwashin taimaka wa Najeriya wajen kawo zaman lafiya.
Wani jami’in kasar Ingila, Sam Waldock, ya ce sun shirya taimaka wa Najeriya, Waldock ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci Gwamna Aminu Tambuwal. Dazu aka ji Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya na kiran a ba kowa damar yin addini, a kyale mata su sanya Hijabi ba tare da wata tsangwama ba.
A matsayinsa na shugaban majalisar kolin addinin Musulunci, Sultan ya ce dole ne tsarin mulki ya ba Musulmai damar rike addininsu muddin ba su taba kowa ba.