Babban mai shiga Tsakani na Sudan, Fadlallah Burma, wanda shine mukaddashin shugaban jam’iyyar Umma a kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an cimma yarjejeniyar maido da Hamdock kan mukaminsa sakamakon ganawa tsakanin Janar din da Hamdok da kuma jam’iyyun siyasa na kasar da kungiyoyin fararen hula.
Wata kungiyar masu shiga tsakani ta Sudan da ta kunshi malaman manyan makarantu da ‘yan siyasa, wadanda tun da aka fara rikicin kasar suka shiga tattaunawa ne suka fitar da sanarwar yarjejeniyar wacce kuma ta bama hamdak damar zama sugaban gwamnati.
A wani labarin na daban kuma Jami’an Tsaro a kasar Sudan sun harbe mutane 15 har lahira daga cikin masu zanga zangar adawa da juyin mulkin da soji suka yi a watan jiya, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban daban.
Kungiyar kwararrun ma’akatan kasar tace kisan da aka yiwa masu zanga zangar ya dada karfafa su, saboda haka ba zasu bada kofar tattaunawa ko hadin kai ko kuma watsi da bukatun su ba wajen ganin sojojin sun bar karagar mulki.
Masu zanga zangar sun mamaye titunan birnin Khartoum duk da katse layukan sadarwa da kafofin intanet da sojojin suka yi.
Masu zanga zangar wadanda akasarin su matasa ne maza da mata, sun ce bukatar su itace mulkin farar hula, yayin da suke kalamun nuna rashin amincewa da jagorancin Janar Abdel Fatah al-Burhan.
Hotunan bidiyo sun nuna wasu masu zanga zangar na jifar jami’an tsaro da duwatsu, yayin da su kuma suke mayar da martini da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasai.