Kungiyar Hamas ta falasdinawa masu gwagwarmaya don kwatar ‘yancin falasdinawa ta yaba da matsayinda kasar Malaysia ta bayyana na goyon bayan al-ummar Falasdinu, bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bada sanarwar cewa nan ba da dadewa ba kasar Malaysia za ta shiga cikin wadanda za su kulla alaka da ita.
Kungiyar ta Hamas ta sanar da haka ne yau Alhamis a cikin wani bayanin da ta fitar, inda ta yaba wa Saifuddin Abdullahi ministan harkokin wajen kasar Malaysia wanda ya fito fili ya karyata labarin da yahudawa suka bayar.
Inda ya ce, kasar Malaysia ba za ta taba barin al-ummar falasdinu ba, kuma za ta ci gaba da goyon bayan su har zuwa samun nasara a kan yahudawa yan mamaya.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a babban taron makon hadin kan al’ummar musulmi da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tehran, wanda masana da malamai daga sassa daban-daban na duniya suke halarta kai tsaye a dakin taron, yayin da kuma wasu suke halarta ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, mahalarta taron sun ce manzon Allah shi ne malamin kur’ani na farko.