Wakilinmu dake Kaduna ya ziyarci tashar jirgin kasa da ke Rigasa a Kaduna ga kuma ya aiko mana da rahoton halin d aake ciki a yanzun.
Wakilin namu dai ya shaida mana cewa zuwa yanzu al’umma suna cikin halin dari dari da kuma tsoro tun bayan da aka samu matsalar kokarin kai hari ga jirgin kasan.
Jirgin kasan dai dake jigilar hanyar Abuja-Kaduna an tabbatar yana dauke da tsohon sanatan kaduna ta tsakiya sanata shehu sani.
Fasinjojin jirgin sun tsallake rijiya da baya ne bayan namijin kokarin da direban jirgin yayinna canjawa jirgin hanya.
A wani labarin na daban gwamnatin Najeriya ta ce ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa mai suna Sunday Adeyemo – wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
Da yake bayani yayin wani taron manema labarai a ofishinsa dake a Abuja ranar Juma’a, ministan ya ce wani kwamati da gwamnati ta kafa ya gano cewa Igboho na da alaƙa da ayyukan Boko Haram bayan ya karɓi kuɗi daga wasu da kotu ta ɗaure a Hadeddiyar Daular Larabawa kan bai wa ƙungiyar tallafi.
Ministan ya ce Igboho ya yi amfani da kamfaninsa mai suna Adesun International Concept Ltd don karɓar kuɗi kuma ya tura naira miliyan 12 ga kamfanin Abbal Bako & Sons, inda ya yi tuni da cewa kamfanin Abbal Bako & Sons da dillalinsa Abdullahi Umar Usman na cikin waɗanda ake zargi a binciken ɗaukar nauyin ta’addanci,”