Da alama akwai fiye da dalili daya na abinda yasa har aka kai ga korar Sheikh Khalid daga limancin Masallacin Apo da ke Abuja Lauretta Onochie, wata hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, ta yi karin haske kan lamarin Onochie a ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu, ta bayyana cewa an kore shi ne saboda hudubarsa ta zuga, ba lallai saboda ya soki ubangidanta ba.
Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta yi magana kan korarren limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Khalid, wanda aka kora bayan wata huduba da ta janyo cece-kuce a cikin kwanakin nan.
Ta wallafar a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 3 ga Afrilu inda ta gabatar da nau’ikan rahotan guda biyu kan makomar malamin addinin Islama da kuma abin da ya kai ga korar shi daga limanci.
Da farko ta musanta labarin da ake yadawa inda aka ce an dakatar da Sheikh Khalid ne saboda sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin tsaro.
Sai Onochie ta ba da tabbacin abin da ta fahimta a matsayin gaskiyar lamari kan korar limamin: An kori limamin ne saboda wa’azinsa na iya kawo tashin-tashina.
Ta alakanta gaskiyar lamarin ga abinda Sanata Saidu Dansadau ya sanar a matsayin dalilin sallamar limamin.
Ga wallafarta ta Twitter: Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu.
A wani labari na daban, tsohon babban limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce korarsa da kwamitin gudanarwa na masallacin ya yi, wata sadaukarwa ce da ya zama dole ya yi domin talakawan da ke cikin wahala da kuma fadin gaskiya ga masu mulki.
Sheikh Khalid ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard a Abuja ranar Litinin da daddare, inda ya kara da cewa korar tasa bai girgiza shi ba.
Vanguard ta ruwaito cewa, ya kara da bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na wani sabon masallacin Juma’a da ke bayan kwatas din babban bankin Najeriya (CBN), Abuja, ya nada shi ya jagoranci jama’a daga ranar Juma’a 8 ga Afrilu.