Musanta rahoton da gwamnatin Mali tayi dai ya nuna rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnati da kuma ma’aikatar addinin kasar.
Akwai dai ‘yan kasar Mali da dama dake kallon gudanar da tattaunawa a matsayin daya daga cikin hanyoyin kawo karshen tashin hankalin da ya barke a kasar tun shekarar 2012, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu dubban da muhallansu.
Sai dai Faransa, wadda ta kaiwa Mali dauki a shekarar 2013, ta dade tana kallon tattaunawa da kungiyoyi masu da’awar jihadi a matsayin abin tirr.
A wani labarin na daban faransa ta fara janye dakarunta na Barkhane daga garin Kidal da ke arewacin kasar, tare da mika sansanoninsu ga dakarun Majalisar Dinkin Duniya wato Minusma wadanda za su yi aiki kafada-da-kafada da sojojin kasar ta Mali.
Tun cikin watan yunin da ya gabata ne Faransa ta sanar da shirin fara janye wasu daga cikin dakarunta daga Kidal, Tumbuktu da kuma Tissalit, matakin da ke tabbatar da alkawarin da shugaba Emmanuel Macron ya yi na rage yawan dakarun sama da dubu 5 zuwa dubu 2 da 500 ko kuma dubu 3 kafin shekara ta 2023.
Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa ya ce za a kammala aikin janye dakarun ne a cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Rage yawan dakarun a daidai lokacin da Mali ke fama da matsalar tsaro, mataki ne da ya yi matukar fusata mahukuntan birnin Bamako, inda Firaminista Choguel Maiga ya zargi Faransa da yin gaban kanta wajen daukar wannan mataki.