Gwamnatin rikon kwariyar kasar Chadi ta mayar da martani biyo bayan zargin ta tareda shigar da kara zuwa kotun hukunta manyan laifuka da wasu kungiyoyi suka yi na cewa kamata a gudanar da bincike dangane da kisan mayakan kungiyar yan tawayen FACT da wasu farraren hula da ake zargin dakarun kasar Chadi da aikatawa bayan mutuwar tsohon Shugaban kasar Idriss Deby.
Ministan sadarwa na kasar ta Chadi Aberaman Koulamallah wanda ke da mukamin mai magana da yahun gwamnatin kasar ya bayyana cewa ana kokarin shafawa hukumomin kasar kashin kaji ne, jami’in ya bayyana cewa kungiyoyi da dama ne suka ziyarci fursunoni dake tsare yanzu haka, suna cikin koshin lafiya, banda haka, batun kisan farraren hula ba gaskiya bane.
Gwamnatin rikon kwariyar Chadi na ci gaba da musanta wannan zargi da kungiyoyi ke yi mata,ta kuma bayyana cewa ta na a shirye don ganawa da duk masu bukata daga cikin dama wajen kasar ta Chadi.
Hakan yana zuwa a kasar ta chadi bayan kisan tsohon zababben shugaban kasar ta chadi wanda daga bayan hakan gwamnatin soji karkashin jagorancin dan tsohon shugaban kasan ta karbi ragamar shugabancin kasar ta chadi wacce take cikin jumlar kasashen yammacin afirka.
Ana zargin kasashen waje musamman faransa a manakisar kashe tsohon zababben shugaban kasar na chadi gami da kunna wutar rikicin cikin gida a kasar ta chadi wanda zuwa yanzu yaki ci yaki cinyewa.
Al’ummar afirka daga bangarori da dama suna ta kira a katse hannayen kasashen ketare daga gudanarwar kasashen afirka domin a cewar afirkawa kasashen ketare musamman na turawa sune babban dalilin da yasa aka rasa tsaro gami da tsarin dimokoradiyya mai dorewa a nahiyar a afirka.
Bincike ya tabbatar da cewa babban abinda yake shigo da turawan yammacin afirka nahiyar afirka baya rasa nasaba da dinbin arzikin da Allah ya horewa nahiyar ta afirka wanda aka tabbatar kasashen turawa suna shiga nahiyar ta afirka ne domin satar aarzikin da ke dankare a nahiyar.