Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da rahoton da ta ciyo bashin Naira biliyan 36 a cikin watanni shida da suka gabata, inda ta bayyana rahoton a matsayin karya da yaudara.
Gwamnatin ta fayyace cewa a zahiri tana biyan bashin kusan sau uku da gwamnatin da ta shude ta dauka saboda faduwar darajar Naira.
Hakan na kunshe ne a cikin wani martani da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, Mukhtar Ahmed ya fitar, inda ya ce ko shakka babu sauyin canjin kudi zai yi tasiri wajen biyan bashin da aka gada.
Duba nan:
- Meyasa Sayyid Hassan Nasrallah yake da muhimmanci ga duniya?
- Najeriya za ta shiga BRICS a daidai lokacin da ya dace – Minista
Gwamnatin ta bayyana cewa bashin da aka gada daga gwamnatin da ta gabata, ya kunshi lamuni na dogon lokaci. “Wadannan alkawurran bayar da lamuni da suka hada da shirye-shiryen Bankin Duniya kamar su AGILE, SURWASH, da ACRESAL, duk an amince da su a zamanin gwamnatin da ta gabata” Kwamishinan ya ci gaba da bayyana hakan.
Yayin da yake jaddada cewa babu wani sabon rance da aka karbo a karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ya ce karuwar karbar rancen, ya zuwa kashi na biyu na shekarar 2024, na da nasaba da faduwar darajar Naira.
Ya kara da cewa: “Yarjejeniyar rancen da gwamnatocin baya suka yi, dangane da canjin kudi na ₦415-₦480 zuwa dala, yanzu Naira ta yi kasa da ₦1,600 zuwa dala, wanda hakan ya rubanya darajar wadannan basussukan a cikin kasar.
Gwamnatin jihar Kaduna, a cewar kwamishinan, ta kuma nuna rashin jin dadin ta da Sahara Reporters saboda rashin neman karin haske kafin buga rahoton. Ya zargi dandalin da yada labaran karya ta hanyar “ta’addanci na dijital” da kuma biyan bukatun waje ta hanyar yunƙurin janye hankali daga binciken da ake yi na rashin sarrafa kudi a karkashin tsohuwar gwamnatin.
Kwamishinan ya kara da cewa, duk da rashin sahihan rahotannin da aka samu, gwamnati na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya a kan basussuka da kuma tsarin kudi, tare da mai da hankali kan inganta tattalin arzikin jihar ba tare da kara wasu sabbin matsalolin kudi ba.
“Ta (gwamnatin jihar) ta sake jaddada aniyar ta na hukunta wadanda ke da hannu wajen karkatar da dukiyar jihar, inda ta sha alwashin mayar da Kaduna matsayi domin amfanin al’ummarta,” Ahmed ya jaddada.