Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin gwamnatin Soja, Dominic Oneya, ya rigamu gidan gaskiya yana mai shekara 73. Hadimin gwamnatin jihar, Abubakar Aminu Ibrahim, ya bayyana haka a jawabin da ya sake ranar Alhamis.
Majiyoyi daga iyalansa sun bayyana cewa tsohon Sojan ya mutu ne a gidansa dake Agbarho karamar hukumar Effurun ta jihar Delta, rahoton Tribune.
Sun kara da cewa ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya saboda ko makon da ya gabata ya tafi Abuja. Oneya, ya kasance gwamnan Kano tsakanin Agustan 1996 da Agustan 1998 lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
Bayan haka kuma, ya kasance gwamnan jihar Benue tsakanin Agustan 1998 da Mayun 1999. Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Abacha ya kwanta dama.
A wani labarin na daban tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta mayar da kakkusar martani dangane da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa kan kasar Syria, da kuma yadda duniya ta yi gum da bakinta kan hakan.
Bayanin na kungiyar Hizbullah ya ce, Isra’ila tana yin amfani da damar da ta samu wajen aikata abin da ta ga dama, ba tare da wani ko wata kasa ta isa ta ce uffan ba, saboda goyon bayan da take da shi daga gwamnatin Amurka, da hakan ya hada har da kai hare-hare a kan kasashen da ta ga dama.
Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Lebanon wajen kai wa kasar Syria hari a jiya Alhamis, amma har yanzu babu wani martani daga bangarori na kasa da kasa kan hakan.
A jiya Alhamis ne dai Isra’ila ta kai hare-hare a yankin Qusair da ke cikin gundumar Homs a kasar Syria, inda ta harba makamai masu linzami a kan wasu wurare na sojin kasar, amma makaman kariya na rundunar sojin kasar at Syria sun kakkabo dukkanin makaman da Isra’ila ta harba.