Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce ‘yan Najeriya za su fara biyan sabon kuɗin haraji nan gaba.
Da take magana ranar Litinin yayin taron jin ra’ayin jama’a kan Ƙudirin Dokar Kuɗi ta 2021 (Finance Bill 2021), Zainab ta faɗa wa kwamatin kuɗi na Majalisar Wakilai cewa matakin na ƙunshe ne cikin dokar.
“Yayin da waɗan nan lamurra ke buƙatar ƙarin haraji a kan wasu harkokin kasuwanci da wasu ɗaiɗaikun mutane da ma’aikatu, wannan gwamnatin za ta ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ƙungiyoyin al’umma,” a cewarta.
Sai dai ta faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa ya yi wuri a fayyace sashen da za a ƙara wa harajin – ko dai a kan harajin sayen kayayyakin yau da kullum na VAT ko kuma harajin shigo da kaya na Stamp Duty.
Ta ƙara da cewa wajibi ne Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin samunta daga man fetur domin gudanar da manyan ayyuka.
A cewarta, ya zuwa Satumban 2021 harajin da gwamnati ta karɓa ya kai naira tiriliyan 4.56, inda aka samu kashi 75 cikin 100 na abin da ake nema. Haka nan, an samu tiriliyan 1.31 na harajin da ba na man fetur ba – kashi 117 cikin 100 kenan na abin da ake nema.
Sai dai ta ce gwamnati za ta ƙara azama wajen ƙara haraji kan lemukan gwangwani kamar barasa da lemon kwalaba da taba sigari domin gudanar da ayyuka a fannin ilimi da lafiya da sauransu.