Gwamnan Jihar Zamfara da Najeriya ya sanar da sauke manyan Sarakunan Jihar guda biyu da Magajin Gari guda saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe ta.
Sanarwar dake dauke da sanya hannu Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan tace an kuma sauke Suleiman Ibrahim Danyabi a matsayin Magajin Garin Birni Tsaba.
Sanarwar tace an dauki matakin sauke Sarakunan ne bayan taron majalisar zartarwa wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar Hassan Nasiha ya jagoranta wanda ya amince da shawarwarin wani kwamitin bincike da ya gano hannun wadannan Sarakuna cikin matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Kafin dai wannan lokaci an dakatar da wadannan Sarakunan daga aiki saboda zargin da ake musu.
A wani labarin na daban Hukumar ‘Yan Sandan farin kaya ta DSS a Najeriya ta bayyana gano shirin kai hari akan wuraren ibada da wuraren shakatawa da kuma wasu kadarorin gwamnati musamman lokacin bikin Sallah da bayan sa.
Jami’in ya bukaci jama’a da su zuba ido domin lura da abubuwan da suke faruwa a yankunan su, yayin da suke gudanar da harkokin su na yau da kullum, tare da gabatarwa jami’an tsaro da bayanan duk wani abinda basu gamsu da shi ba a yankunan su.