Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya hori mambobin sabuwar majalisar zartaswa ta jihar da su yi amfani da gogewarsu, kwarewarsu da kuma damar da suka samu wajen hidimta wa al’ummar jihar a maimakon amfani da damar wajen azurta kawukansu.
Yana mai cewa, kamar yadda tun farko mulkinsa ke sanya ido kan yadda ma’aikatu ke tafiyar da ayyuka da ririta dukiyar al’umma, a yanzu din ma zai ci gaba da yin hakan ba wai don yin katsalandan wa kwamishinoni ba, domin tabbatar da manufofin da gwamnatinsa ta sanya a gaba na yin gaskiya da adalci da bunkasa jihar.
Bala ya bayanin halan a lokacin da ke rantsar da sabbin kwamishinoni 21 tare da sakataren gwamnatin jiha da kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnati domin su kama aiki gadan-gadan kamar yadda doka ta shimfida.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar 9 ga watan Yuni ne gwamnan ya rushe mambobin majalisar zartarwa na jihar da suka kunshi sakataren gwamnatin jihar (SSG), shugaban ma’aikatan gidan gwamnati (CoS) da kuma dukkanin masu ba shi shawara na musamman a fannoni daban-daban illa mutum hudu daga cikinsu da ya bari.
A cikin jawabinsa, jim kadan bayan da Babban Jojin Jihar Bauchi, Justice Rabi Talatu Umar ta rantsar da mambobin majalisar zantarwar, Bala Muhamamd, ya ce zabin da aka musu an yi ne bisa cancanta da dacewa, don haka ne ya nemi su baiwa mara da kunya ta hanyar gudanar da aikin da zai ciyar da Jihar Bauchi gaba da al’ummarta.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa wadanda suka sha rantsuwar kama aikin sun hada da Barista Ibrahim Kashim a matsayin SSG; sai kuma Dakta Aminu Hassan Gamawa a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati (CoS); Bashir Yau a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, sai kuma Pharmacist Samaila Adamu Burga a matsayin babban sakataren musamman na gwamna (PPS) tare da kwamishinoni 21 wadanda nan take ya raba musu ma’aikatun da za su yi aikinsu a ciki.