Gwamnan Borno Babagana Zulum ya yaba da halin da aka cimma ta fuskar tsaro a wannan jiha, gwamnan yayin jawabin sabuwar shekara a yau asabar a Maiduguri ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ayukan da ta saka gaba musaman a bangaren sake dawo da tsaro.
A karshe Gwamnan ya bayyana cewa mudin aka rufe idanun ganin abubuwan dake faruwa a sansanonin yan gudun hijira ,za a wayi gari,matasa za su shiga wani mauyacin hali da suka hada da shan barasa,ayukan karuwanci da sauren abubuwa marar sa kyau.
A wani labarin nja daban Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum yau ya ziyarci garin Damasak dake kusa da Tafkin Chadi domin karfafawa mutanen yankin ci gaba da gudanar da aikin noma a daidai lokacin da damina ta fara zama a yankin.
Yayin ziyarar Zulum ya bada umurnin tattara bayanan iyalai 3,000 da za’a baiwa tallafin kayan aikin noma da suka hada da ingantaccen iri da takin zamani da injin din ban ruwa da kuma maganin kashe kwari domin ganin sun koma gonakin su da taimakon jami’an sojin Najeriya.
Mai magana da yawun Gwamnan Isa Gusau yace wannan shine karo na 2 da iyalai 3,000 zasu ci gajiyar irin wannan shirin na samun tallafin kayan noman rani da na damina, kuma an shirya kowanne iyali guda na dauke da mutane akalla 6 abinda ke nuna cewar mutane 18,000 zasu amfana da shirin.
A watan Janairun da ya gabata, Gwamnan da ya ziyarci Damasak ya sanya ido wajen raba iri da takin zamani da maganin kashe kwari da injin din ban ruwa da kuma naira N5,000 ga manoma 1,200 wadanda yanzu haka ke girbe amfanin gonakin su da suka hada da albasa da shinkafa da kuma tattasai.
Yayin ziyarar sa ta yau, Gwamna Zulum ya zagaya wasu daga cikin gonakin dake yankin domin ganewa idan sa halin da ake ciki inda ya bayyana gamsuwar sa da irin ci gaban da aka samu.
Gwamnan ya sha alwashin ci gaba da tallafawa manoman domin ganin sun ci gaba da ayyuka a gonakin su bayan kwashe shekaru 6 ba’a aikin noma saboda rikicin boko haram da ya addabi yankin a shekarar 2014.