Gwamna Nasir El-Rufai da wasu sun yi wa Gwamnatin PDP zanga-zanga a 2012.
Gwamnan ya soki karin kudin man fetur da Goodluck Jonathan ya yi.
A yau, Gwamnan na Kaduna ya na yaki da masu yi masa zanga-zanga A lokacin da gwamnatin Goodluck Jonathan take mulki tsakanin Mayun 2010 zuwa Mayun 2015,
Gwamna Nasir El-Rufai ya na cikin manyan ‘yan adawarta. Malam Nasir El-Rufai da wasu ‘yan adawa a lokacin, sun jagoranci zanga-zangar OccupyNaija sa’ilin da gwamnatin tarayya ta kara kudin man fetur.
Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya zama gwamna a 2015 sune ‘yan gaba-gaba, tare da tsohon Sanata Dino Melaye da tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode.
A wajen zanga-zangar, za a ji Sanata Dino Melaye ya na cewa: “Zan mika abin magana zuwa ga Malam Nasir El-Rufai, bayan jawabinsa, za mu saurari Femi Fani-Kayode, daga nan sai mu wuce kasuwar Wuse.”
Sai aka yi shewa! Da tsohon Ministan birnin tarayyar ya karbi abin magana, sai ya soki gwamnati mai-ci a lokacin, ya nuna ya kamata a rika saida litar man fetur a kan N40 rak: “Mutanen Najeriya masu daraja! Ina so in yaba wa kokarinku na tsaya wa tsayin-daka.”
“Za mu cigaba da yakar wannan gwamnati, har sai tayi abin da ya kamata.” Gwamna Nasir El-Rufai.
Abin da ya dace shi ne, gwamnati ta rage kudin da suke kashewa, a tabbatar da matatunmu sun dawo aiki.” “Domin mu saye man fetur, ba ma a kan N65 ba, a kan N40!”
“Yanzu za mu wuce zuwa kasuwar Wuse, sai mu zarce filin taron ‘Eagle square’” Daga nan kuma Femi Fani-Kayode ya karbi abin magana, ya yi kaca-kaca da gwamnatin PDP.
Amma daga baya, Fani-Kayode ya bar APC, ya koma PDP.
A kwanakin baya ne kuma aka ji Yahaya Bello ya fito ya na cewa Femi Fani-Kayode zai dawo APC, duk da irin sukar da ya rika yi wa gwamnatin Buhari.