Kotu ta saka ranar Litinin domin soma sauraren shari’ar Abba gida-gida da Gawuna
A ranar 20 ga watan Satumba ne Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano inda ta ayyana Jam’iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara a zaben na watan Maris din 2023.
A watan Satumba ne kotu ta kwace nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben Maris din 2023. Hoto/Others
Kotun Daukaka Kara ta Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta saka ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta soma sauraren karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kan kwace masa zabe da kotu ta yi.
A ranar 20 ga watan Satumba ne Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano inda ta ayyana Jam’iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara a zaben na watan Maris din 2023.
A hukuncin da kotun mai tawagar alkalai uku ta yi a baya ta ce a kwace shaidar cin zabe da INEC ta bai wa Abba tare da umartar cewa a mika wa Nasiru Yusuf Gawuna ita.
Kotun ta cire kuri’a 165,663 daga kuri’un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri’un 165,663 hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.
Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya shigar da kara inda yake kalubalantar hukuncin kotun.
Tun da farko a zaben da aka yi a watan Maris din 2023 Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, sai kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC ya samu 890,705.
Source: TRTHAUSA