Mayakan Boko Haram sun kai hari kan garin Geidam, da ke jihar Yobe, inda suka kutsa cikin garin a daren Larabar da ta gabata.
Bayanai sun ce ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun afkawa wasu daga cikin mazauna yankin gabashin garin na Geidam ne, inda suka kona wata makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati, bayan kashe mutum daya a harabar makarantar.
Wata majiyar da Daily Trust ta ruwaito, ta bayyana cewarmayakan na Boko Haram sun kuma kai hari kan wani gidan mata masu zaman kansu a garin an Geidam inda suka kashe mutane akalla 10.
A wani labarin na daban kuma a kalla sojojin Najeriya 13 ake fargabar sun rasa rayukansu sakamakon farmakin da mayakan ISWAP suka kai musu a arewa maso gabashin kasar.
Bayanai sun ce tawagar dakarun Najeriya sun gamu da turjiyar ce yayin da suke kan hanyar zuwa sansaninsu dake Buni Yadi.
Sai dai cikin sanarwar da fitar ranar Lahadi a hukumance, rundunar sojin Najeriya tace sojanta 1 ne kawai ya mutu yayin fafatawar da suka yi da ‘yan ta’addan a ranar Asabar, kuma sun samu nasarar kashe 28 daga cikinsu.
A shekarar 2016 kungiyar Boko Haram ta rabu zuwa gida biyu, abinda ya bada damar kafuwar mayakan ISWAP da suka yiwa kungiyar IS mubaya’a.