Alhaji Nasiru Gawuna, mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, ya taya zababben shugaban kasa, Sanata Bola Tinubu, da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, murnar nasarar da suka samu a zaben ranar Asabar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Malam Hassan Musa-Fagge ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Gawuna ya kuma yabawa magoya bayan jam’iyyar da suka bayar da ruwan kuri’unsu ga ‘yan takarar jam’iyyar, ya sake yin kira gare su da su sake fitowa su kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.
“Kun fito a baya kuma mun yi imanin za ku sake yin hakan a cikin tsarin siyasa na zaman lafiya don tabbatar da nasarar ‘yan takararmu masu neman mukamai daban-daban a jihar” in ji shi.
A wani labarin na daban bayanai na nuna cewa, a ’yan shekarun baya-bayan nan, ofisoshin kwastam na kasar Sin, sun samu babban ci gaba wajen sa kaimi ga gudanar da harkokin kasuwanci a kan iyakokin kasar.
Wani jami’in hukumar kwastam mai suna Zhao Zenglian, ya shaida wa taron manema labarai cewa, lokacin da hukumar ke dauka wajen tantance kayayyakin da ake shigo da fitar da su, ya ragu sosai.
Zhao ya ce a shekarar 2022, baki dayan lokacin da aka dauka wajen shigo da ma fitar da kayayyaki don kammala aikin kwastam, ya kai sa’o’i 32.02 da sa’o’i 1.03, bi da bi, raguwar kashi 67.1 da kashi 91.6 kan na shekarar 2017.
Sauran abubuwan da aka samu ci gaba, sun hada da raguwar farashi da takaita hanyoyin shigo da kaya da ma fitarwa, da nufin rage kudaden da kamfanoni ke kashewa, da kuma biyan bukatun kasuwancin su.
Taron manema labarai na ranar Talata ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da shawarwari 148 da wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar suka gabatar da kuma shawarwari 141 da mambobin kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin suka bayar a bara. (Ibrahim Yaya)
Source:LeadershipHausa