Masu bincike a jami’ar Oxford sun fitar da sanarwar gano wani sabon naucin kwayar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki a Kasar Netherlands.
Kazalika binciken ya kuma gano bayan fara shan magani, warkewar masu dauke da kwayar VB ya banbanta da na wadanda aka sani a da.
Sai dai a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, Chris Wymant wani kwararre a jami’ar ta Oxford ya ce kowa yayi karatun ta natsu da bullar sabon nau’in cutar ta HIV, bugu da kari, ya ce ba wani abin daga hankali.
Cutar ta HIV dai ta bulla ne a karshen shekarar 1980 a Kasar Netherlands, sai dai adadin yaduwarshi ya zaftare a cikin shekarar 2010 kamar yadda masu bincike suka bayyana.
Cutar ta HIV ta shafe gomman shekaru tana bazuwa a kasar da al’ummarta suka bayyana kwanciyar hankali da zaman cutar a tattare dasu ganin yadda magungunan da ke akwai na karya kaifin ta.
Wannan rahoto dai na zuwa ne a daidai lokaci da duniya ke fama da annobar coronavirus da yayi ta’adi a bangarorin rayuwa dabam dabam na duniya.