Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Alhamis, wanda ya tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ganduje, a wata sanarwa dauke da babban sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, ya ce hukuncin ya koma kan duk wani ikirarin jam’iyyun siyasa na adawa suka yi na cewa an yi amfani da kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa domin goyon bayan Shugaba Tinubu da APC.
Ganduje ya bayyana cewa sakamakon hukuncin kotun koli a yanzu zai bayar da dama ga shugaba Tinubu ya maida hankali wajen aiwatar da ajandar jam’iyyar APC domin amfanar ‘yan Nijeriya.
Ganduje ya yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da na Labour Party (LP), Peter Obi, da su hada kai da Shugaba Tinubu, domin ci gaban kasar nan.
“Nijeriya guda daya muke fata, hakkinmu ne a matsayinmu na ’yan kishin kasa mu hada dukiyoyinmu domin ciyar da kasa gaba, ina taya Atiku da Obi murna kan yakin da suka yi na tsawaita mulkin dimokuradiyya da doka.
“Wannan ita ce dimokuradiyya. Nasarar Tinubu wata nasara ce ga mulkin dimokuradiyya a kasar nan. Har yanzu akwai sauran damar da Obi da Atiku za su iya bayarwa wajen shugabancin kasa bayan wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a 2031,” in ji shi.
Don haka Ganduje ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa gwamnatin Tinubu baya don samun alfanu.
Source LEADERSHIPHAUSA