Tsohon dan wasan gab ana Kano Pillars Gambo Mohammed ya yi wa ‘Sai Masu Gidan’ kome, amma a wannan karo a matsyain mataimakin mai horar da ‘yan wasa.
Jami’in yada labarai na kungiyar ta Kano Pillars,
Rilwanu Idris Malikawa Garu, shugaban kungiyar Alhaji Surajo Shuaibu Jambul ne suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin Gambo ya koma wannan kungiya a matsayin mai horarwa, la’akari da irin gudummawar da ya ba ta a lokacin yana dan wasa.
Jim kadan bayan an nada shi, Gambo ya kasance a cikin tawagar masu horarwa da ta jagoranci ‘yan wasan kungiyar a wasan da suka karbi bakoncin Plateau United a Kaduna.
A wani labarin na daban kuma Mai horas da Kano Pillars Bafaranshe Emmanuel Lionel Soccoia ya ajiye aikinsa watanni 5 bayan kulla yarjejeniyar shekara 1 da kungiyar a watan Oktoban shekarar 2020.
Lionel ya ce yanzu haka yana bin kungiyar ta Pillars albashin watanni 5 da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 25. Zalika ya koka kan gazawar da kungiyar tayi wajen sama mishi takardar izinin zama domin aiki a Najeriya kamar yadda doka ta tsara, abinda ya sa ofishin jakadancin kasarsa Faransa ya nemi ya koma gida, kasancewar cigaba da zamansa a Najeriya ya saba ka’ida.
Sai dai jami’in hulda da kafafen yada labaran kungiyar ta Pillars Rilwanu Idris Malikawa ya musanta zargin kocin mai murabus na cewar ana yi masa katsalandan.