Gwamnatin Kazakhstan ta ce mutane fiye da 225 suka mutu a rikicin da ya barke a kasar, wanda ya fara daga zanga-zangar lumana a farkon watan Janairu, kan tsadar rayuwa.
Bayan rikidewar zanga-zangar da aka fara zuwa tarzoma da kuma arrangama tsakanin wani gungun mutane masu makamai da jami’an tsaro ne, shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya ayyana dokar ta-baci tare da neman agaji daga wata kungiyar gamayyar sojojin kasa da kasa da ke karkashin jagorancin Rasha.
Da fari dai mutane kusan 50 kawai gwamnatin Kazakstan ta ba da sanarwar sun mutu a rikicin da ya barke, wadanda ta ce 18 jami’an tsaro ne sai kuma ‘yan bindiga 26.
Sai dai a halin da ake ciki, sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar, sun nuna cewar baya ga mutane fiye da 225 da suka halaka, wasu fiye da dubu 2 da 600 ne suka jikkata, 67 daga cikinsu kuma na cikin mawuyacin hali.
A wani labarinn na daban Babban mai shigar da kara na Haiti ya mika bukatar fara tuhumar Firaministan kasar Ariel Henry dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise.
Cikin wata wasika wadda ke matsayin ta 2 da sashen shigar da karar ya gabatarwa gwamnati ya nemi hukumar shige da fice ta kasar ta haramtawa Firaminista Ariel Henry barin kasar a kowanne yanayi.
Wata shaidar baya-bayan nan ta nuna yadda Henry ya yi waya da babban wanda ake zargi da kisan shugaban na Haiti, lokaci kankani bayan farmakin da ya hallaka shugaban.
Wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara ta kasar ta kuma nemi izinin gurfanar da Firaministan don amsa tuhuma dangane da alakarsa da maharan na ranar 6 ga watan Yuli.
Tun a juma’ar da ta gabata babban mai shigar da karar ya aikewa da Firaministan bukatar ganin ya bayyana gaban kotu jiya talata don amsa tambayoyi da ke matsayin kari kan bayyanarsa gaban mahukuntan kasar sa’o’I kalilan bayan kisan shugaba Moise amma kuma yaki mutunta gayyatar.