Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya zabi Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin mataimakiyar sa.
Gwamna Fintiri ya ce an zabe ta ne saboda halayenta na gaskiya da rikon amana da jajircewa da kuma tafiya tare da mata a gwamnati.
A bangaren ta, Farfesa Farauta ta mika godiya ga gwamnan bisa wannan damar da ya bata ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya zabi farfesa mace, Kaletapwa Farauta, a matsayin abokiyar takararsa domin zaben shekarar 2023.
A Wajen Liyafar Bikinta Ya ce ana sa ran za ta yi ayyukanta cikin gaskiya da tsoron Allah, bugu da kari za ta cigaba da aikinta na gida a matsayin matar aure.
“An zabe ta ne bayan lissafi da nazari musamman bukatar dama wa tare da mata a siyasa,” in ji shi.
Gwamna Fintiri ya bukaci jam’iyyun adawa ta hada kai da gwamnatinsa wurin aiki don cigaba da inganta jihar. Jawabin Farfesa Farauta.
A jawabinta, Mrs Farauta, wacce ta bayyana zabinta a matsayin ikon Allah, ta mika godiya ga Mr Fintiri da jam’iyyar PDP saboda damar da aka bata.
Ta bada tabbacin cewa za ta yi aiki tukuru da biyayya da tsoron Allah ta kuma ce: “Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar jam’iyyar mu a zaben da ke tafe.”
An haifi Mrs Farauta ne a ranar 28 a shekarar 1965 a karamar hukumar Numan a jihar Adamawa, ita ce kuma mace ta farko da ta fara zama shugaban jami’a a Arewa maso Gabas a Jami’ar Jihar Adamawa a Mubi.
Source:hausalegitng