Gwamnan jihar Adamawa Ahamdu Umaru Fintiri, ya rantsar da mace ta farko Justis Hafsat AbdulRahman, a matsayar babbar Mai Shari’a kuma alkaliyar-alkalan jihar, ranar Litinin, a gidan gwamnati dake Yola fadar jihar Adamawa.
Haka kuma cikin mutanen da gwamnan ya rantsar sun hada da Ibrahim Sudi da Audu Balami, a matsayin manyan alkalan kotun Shari’ar Musulunci da kotun daukaka kara ta shari’ar gargajiya.
Da yake jawabi jimkadan da rantsarwar gwamna Ahamadu Umaru Fintiri, yace sabbin alkalan-alkalan jihar su na da cikakken ikon gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta ba su, saboda haka zaiyi aiki da su a matsayinsu cikakkun alkalai.
Gwamnan ya kuma yabawa babbar Mai shari’a Hafsat AbdulRahman bisa kwarewa da gogiwa da jajircewar da take dashi, da yace hakan ya kai ga kwarewarta da rike mukamai a fannin shari’a a tsawon shekarun aikin da ta yi.
Ya ci gaba da cewa “gwamnatinmu ta kafa tarihi ta hanyar rantsar da mace a matsayar babbar alkalin-alkalan jiha, nasararta babban ci gaba ne ga mata, hadarin da ‘yancin yara mata ke ciki, ya nuna abune da yanzu akwai kyakkyawar fata.
“Iyaye, idan muna nemawa yayanmu mata hanyar da ta dace, wannan shine ingantaccen wurin da za mu zo, kyakkyawar fata, ‘yanci, gaskiya da kuma aiki tukuru, kallafawa, amana da adalci.
“Rantsar da ku, yana daga shawarwarin da majalisar shari’a ta NJC ta bamu, shawarar na su wata alamace ta aikinmu ya dace, aiki ne wanda NCJ ke da ikon nada manyan masu shari’a” inji Fintiri.
Da take jawabin godiya a madadin alkalan, Mai shari’a Hafsat AbdulRahman, ta yabawa gwamnan bisa gaggawar amincewa da shawarwarin majalisar shari’a ta kasa (NCJ).
Justis Hafsat, ta kuma tabbatar da cewa za su yi abinda ya dace, domin daukaka matsayin shari’a a jihar da rantsarwar da suka dauka,
Ta kuma yaba da babban gudumuwar da gwamnatin jihar ke ci gaba da bayarwa wajan daukaka matsayin shari’a, musamman ta fuskacin daukan ma’aikata.
Ta ce “daga shekarar 2020 zuwa yanzu, alkalan-alkalan manyan kotuna 10, garan Khadi 3, kotunan daukaka kara da manyan alkalan kotunan shari’ar gargajiya 3, aka nada da rantsar da su” inji Mai shari’a Hafsat.