Wasu matasan Kiristoci a Jihar Filato dake Najeriya sun hada kudi domin sayawa Masallachin juma’ar garin su injin din samar da wutar lantarki ko kuma janereta domin amfani da shi wajen kiran Sallah da kuma wa’azi a cikin watan Ramadana.
Wannan aiki na matasa ya gamu da yabo daga ciki da wajen Jihar Filato musamman a daidai lokacin da gwamnatin Jihar ke ta kokarin ganin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hada kan jama’a domin samun ci gaba.
Jihar Filato ta yi fama da rikicin kabilanci da addini tun daga shekarar 2001, abinda yayi sanadiyar rasa dimbin rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi, yayin da rashin yarda ya fadada tsakanin al’ummar jihar.
Wannan ya sa shugaban kasa na wancan lokaci Olusegun Obasanjo kafa dokar ta baci da dakatar da Gwamnan Jihar Joshua Dariye na wani lokaci, yayin da ya nada Janar Chris Muhammed Ali a matsayin Kantoma na wani lokaci.
Har ya zuwa wannan lokaci akan samu hare hare jifa jifa wadanda ke kaiga rasa rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi a wasu sassan Jihar, duk da kokarin da gwamnatin Simon Lalong ke yi na wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin jihar.