A ranar talata 5 ga watan oktobar shekarar da muke ciki ta 2021 ne muka samu labarin babban malamin addini kirista dinnan kuma wanda ke wa’azin tabbatar da hadin kai tsakanin al’ummomin musulmi da kiristoci, fasto yohanna buru ya kaiwa babban shehin malamin addinin musuluncin nan wanda bai jima da fitowa daga gidan kurkuku ba watau sheikh Ibrahim Yaqoob Alzakzaky ziyara agidan sa dake babban birnin tarayyar Abuja.
Fasto yohanna buru dai yana cikin manyan malamai a bangaren mabiya addinin kirista a najeriya kuma an jima da jiyo duriyar sa dangane da kiran a samu fahimtar juna tsakanin mabiyan addinai mabambanta najeriya.
A bangare daya kuma malam zakzaky ya jima da kiran bangarorin addinai da fahimtoci domin azo a hada kai domin samar da zaman lafiya tsakanin al’ummara najeriya baki daya.
Ziyarar ta fasto yohanna buru tazo ne a dai dai lokacin da gwamnatin najeriya ta hana sheikh zakzzkay fita kasashen ketare domin neman magani dashi da mai dakin sa duk da umarnin da kotu ta bayar na wanke sheikh zakzaky din kuma tare da cewa kundin tsarin mulkin kasa ya bama shehin malamin damar walwala da kuma fita duk inda yake so domin neman lafiya kmamar kowanne dan kasa.
A ziyarar sa fasto yonanna buru ya bayyana takaicin sa bisa \ga wannan mataki na rashin adalchi a gwamnatin najeriyar ta dauka a kan shehin malamin da iyalan sa inda yayi addu’ar Allah ya gaggauta bama shehin malamin lafiya tare da mai dakin tasa malama zinatuddin.
A bangare guda yau laraba 6 ga oktoban 2021 ake sa ran sheikh Ibrahim Zakzaky zai bude taron ‘yan gwagwarmaya na kasa da ksa wanda aka yima tare da tunawa da shahadar Imam Ridha (S.a), wanda za’a gudanar a birnin Tehran na jamhuriyar musulunci ta Iran.
Ana sa ran dai sheikh zakzaky zai bude taron ne da jawabi ta kafar ”skype” inda mahalarta daga kasashe mabambanta wadanda suka fito daga nahoyoyin turai, asiya da afirka zasu saurara.