Wasu fasinjojin dake tafiya ta jirgin kasa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja dake Najeriya sun tsallake rijiya da baya sakamakon harin da ake zargin ‘yan bindiga sun kai musu wajen amfani da na’urorin dake fashewa tare da bindigogi akan jirgin da suke ciki a yammacin laraba
Sanata Shehu Sani, na daya daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin yau da safe, lokacin da ya sake taka wani abu mai kama da nakiya, kafin yayi sa’ar wucewa.
A tattaunawar da yayi da wakilian mu, tsohon Dan Majalisar Dattawan ya bayyana harin a matsayin tashin hankali, wanda ya jefa fasinjojin jirgin cikin mawuyacin hali kafin su kubuta.
Shugaban Hukumar kula da sufurin jiragen kasar Najeriya Fidet Okhiria ya tabbatar da samun matsalar amma yace ya zuwa wannan lokaci ba zasu iya cewa ‘Yan ta’adda ne suka kai harin ba, har sai abinda bincike ya nuna.
Fidet ya danganta matsalar da aka samu da bata gari da kan kai hari akan layin dogon a hirar da yayi da Jaridar Daily Trust.
Shugaban Hukumar yace suna iya bakin kokarin su wajen gyara hanyar da ta baci, kuma da zaran sun kamala sufurin jiragen zai ci gaba.
Abubakar ya bayyana cewar mutane da dama na amfani da addini wajen mummunar fassara domin biyan bukatar kan su, saboda babu wanda ke tankwasa su, musamman daga cikin manyan addinan kasar guda biyu.
Sarkin Musulmin ya bayyana wannan matsalar a matsayin babbar kalubalen da ya addabe su, saboda haka ya dace a rungumi shirin bayar da ilimi domin kawar da matsalar tsatsauran ra’ayi a cikin al’umma.
Abubakar ya bukaci hukumomin Najeriya da su dauki duk matakin da ya dace wajen hana masu tsatsauran ra’ayi karbe ragamar tafiyar da kasar ta hanyar amfani da addini da kuma matakan tsaro.
Daga karshe Sarkin Musulmi ya bayyana matsalar rashin amfani da shawarwarin masana wajen shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya a matsayin babban kuskuren da ya sanya Najeriya a cikin yanayin da ta samu kan ta ayau.
Shugaban sojin kasa na Najeriya Lafatanar Janar Faruk Yahya ya bayyana cewar ana iya shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar muddin kowa ya bada gudumawar da ake bukata.