Faransa na karbar bakuncin taron ministocin kasashen Turai domin tattauna hanyoyin hana bakin haure tsallaka mashigin ruwan dake tsakaninta da Birtaniya cikin kananan kwale-kwalesai dai ba ta gayyaci Birtaniyar ba, wadda takkadama ta kaure tsakaninsu kan batun a makon da ya kare.
An kira taron ne biyo bayan mutuwar mutane 27 a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da suke yunkurin tsallakawa daga Faransa zuwa Ingila a cikin wani jirgin ruwa da ake hurawa iska, wanda ya sace cikin teku saboda tsananin sanyi.
Yanzu haka dai matsalar bakin hauren ta janyo cece-kuce tsakanin Birtaniya da Faransa, bayan da fira minista Boris Johnson ya wallafa wasikar da ya aikewa shugaba Emmanuel Macron a shafinsa na Twitter kan yadda za a shawo kan matsalar.
A wani labarin na daban shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce yayi mamakin yadda Prime ministan Birtaniya Boris Johnson ya tunkari matsalar bakin haure dake Kutsawa Turai ta kasar, inda ya ce bai kamata jagororin al’umma su rika musayar bayanai ta kafafen sada zumunta ba.Wannan na zuwa ne bayan da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya wallafa wani bangare na wasikar da ya aike wa Emmanuel Macron din a shafin sa na Twitter.
Shugaban na Faransa Emmanuel Macron na wadannan kalamai ne yayin ziyarar da ya kai wa Fafaroma Francis, inda ya ce abin mamaki ne yadda Prime ministan Birtaniya ya zabi yin bayani kan matsayar kasar ta shafinsa na Twitter a maimakon neman gudanar da zama na musamman, la’akari da girman matsalar.
Ya ce babu dalilin da zai sanya Boris Johnson ya wallafa sakon wasikar da ya aike masa a shafinsa na Twitter, yana bukatar Faransa ta mayar da bakin hauren da suka yi nasarar shiga Birtaniya ta kasar, abin da ke biyo bayan mutuwar wasu bakin haure 27.
Sai dai tun kafin wannan dambarwa, Ministan harkokin cikin gida na Faransa Gerald Dramanin ya shaidawa takwarar sa ta Burtaniya Priti Patel cewa ba’a gayyace shi tattaunawar da aka shirya gudanarwa a karshen mako kan batun matsalar bakin hauren da aka shirya gudanarwa da dukkanin ministocin kasashen turai ba.
To amma da ya ke mayar da martani Prime ministan Birtaniya Boris Johnson ya ce ba zai taba yin dana sanin wallafa bayanan da ya yi a shafin sa na Twitter, wadda ke neman Faransa ta mayar da bakin hauren da suka bi kasar zuwa Burtaniyan ba, abinda tuni Faransan tace ba mai yiwuwa bane.