Ma’aikatar harakokin wajen kasar Faransa ta ce, ta karbi korar jakadanta da mahukuntan mulkin sojin Mali suka yi, tare da jaddada matsayinta kan ci gaba da yakin da take da ayyukan ta’addanci.
Har ila yau, mahukuntan Paris sun jaddada goyon baya da zumuncinsu ga abokan huldarsu na kasashen Turai dake kasar Mali, musamman kasar Danemark”, wadda ba da jimawa ba dakarunta suka isa kasar, karkashin rundunar kasashen duniya dake yaki da ayyukan ta’addanci wato Takuba, da mahukuntan na Bamako suka kora saboda dalilan na kashin kansu.
Har ila yau ma’aikatar wajen ta Faransa ta jaddada goyon bayanta ga kungiyar gamayyar tattalin arzikin yankin yammacin Afrika (ECOWAS ko Cédéao) da ta kori Mali a cikinta, bisa kokarin da take wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin Sahel.
Mahukuntan mulkin sojin kasar ta Mali dai sun yanke shawarar korar jakadan na Faransa a Mali a cikin wata sanarwa da suka fitar a tashar talabijin din gwamnatin kasar bisa kafa hujja da wata sanarwar da mahukuntan Faransa suka fitar ta cin mutuncin mahukuntan na Mali.
Wannan sanarwa dai ta sake haifar da wata sabuwar takadama tsakanin Mali da Faransa, kasar da ta yi mata mulkin mallaka da tun 2013 ta shiga kasar da aikin soja domin yaki da mayakan dake ikararin jihadi a Mali da ma yankin Sahel.