Enyinnaya Abaribe yace sun yi tarayya da Sanatocin APC a game da batun tsige shugaban kasa Sanatan ya yi raddi ga Fadar Shugaban kasa, yace matsalar tsaro ta tashi daga Arewa maso gabas.
Shugaban marasa rinjayen na majalisar dattawa yace adadinsu ya kai su sauke Shugaban Najeriya.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe, ya yi ikirarin ‘ya ‘yan APC suna tare da su a kan yunkurin tsige shugaban kasa.
Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa Femi Adesina martani bayan hirar da aka yi da shi.
Daily Trust ta kawo wannan rahoto.
Abaribe ya nuna damuwarsa a kan halin rashin tsaron da aka shiga yanzu a Arewacin Najeriya.
‘Dan majalisar adawar ya bayyana cewa daga cikin Sanatocin jam’iyyar APC, akwai da-dama da suke goyon bayan a tunbuke shugaba Muhammadu Buhari.
“Ina tunani wasu sun zauna a Abuja suna cewa ba zai yiwu ‘yan ta’adda su fito daga Arewa maso gabas ba, a wani hali muke ciki a yau? “Kuskure ne wani mutum yace ba mu da adadi (na wadanda za su tunbuke shugaban kasa daga kan mulki).
Wannan ba gaskiya ba ne Mafi yawan Sanatocin APC suna tare da mu. Kuma a daidai lokacin da aka fara, ‘Yan Najeriya za su fahimci kusan kowane Sanata ya gaji.”
Wa’adi ya kawo karshe Daily Trust tace da aka tambayi Sanatan na Abia dalilin neman tsige shugaban kasa alhali wa’adinsa ya zo karshe, sai yace ba za a jira sai an mutu ba.
“Sai mun jira wannan gwamnati ta murkushe kasar nan ko kuwa za mu dauki matakin hanawa ne?”
Bata lokaci ne: Garba Shehu Dazu kun ji labari Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi a dalilin wa’adin da wasu Sanatoci suka ba Muhammadu Buhari na sauke shi daga kan mulki.
Mai magana da yawun bakin shugaban na Najeriya ya yi wa ‘Yan Majalisar dattawan kaca-kaca, ya kira su da birkitattu kuma masu bata lokacinsu a banza.
Source:hausalegitng