Sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa a majalisar dattawa, Elisha Ishaku Abbo, ya bayyana cewa zai kalubalanci hukuncin kotu da ke hana masa takara a zabe mai zuwa Abbo ya bayyana cewa zai daukaka kara a gaban kotun daukaka kasa.
Sanatan na APC ya kuma cewa wadanda suka kore shi daga jam’iyyar ba Jami’an karamar hukuma bane don haka basu da hurumin yin haka.
Sanata Ishaku Abbo mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa a majalisar dokokin tarayya ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotu da ke haramta masa takara a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga hukuncin babban kotun jihar karkashin jagorancin Justis Danladi Mohammed wanda ya haramta masa takara a zabe mai zuwa.
Yayin da yake zartar da hukunci, Justis Mohammed ya riki cewa APC a karamar hukumar Mubi ya arewa ta kori Sanatan a ranar 7 ga watan Oktoba 2022, cewa bai da hurumin tsayawa takara a jam’iyyar. Kotu da ake ganin ita ce gatan talaka ta zama wajen ciniki, Abbo.
A wata hira da Channels TV, Abbo ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wanda aka siye.
Ya koka cewa kotu da ake ganin ita ce gatan talaka ta zama na ciniki.
A cewarsa, hukuncin akwai tangarda saboda wadanda suka kore shi daga jam’iyyar ba jami’an karamar hukuma bane kuma saboda haka babu hujjar kore shi.
Bugu da kari, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin APC, shugaban jam’iyyar na gudunma ne kadai yake da hurumin hukunta dan jam’iyya ba shugaban karamar hukuma ko na jaha ba.
Ya kara da cewar alkalin ya taba ba da umurni da ke hana shugabannin karamar hukumar daga daukar kansu a matsayin Jami’an jam’iyyar.
Abbo ya kuma tabbatarwa da Channels TV cewa zai daukaka kara a kotun daukaka kara sannan ya yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu.
Bakano ya samu babban mukami a gwamnatin Kuros Riba A wani labari na daban, gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya yi garambawul a majalisarsa gabannin kammala wa’adin shugabancinsa.
Gwamnan ya nada sabbin kwamishinoni 12 ciki harda wani Bakano kuma musulmi na farko da ke samun irin wannan babban mukami a jihar.