Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 13 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar da ke neman hana Dr. Abdullahi Ganduje gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya sanya ranar domin ba wa dukkan ɓangarorin damar daidaita takardunsu na kotun. Ƙarar da ƙungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ta shigar, ta ce nadin Ganduje ya saɓawa kundin tsarin mulkin APC tunda shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne.
Ƙungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ƙarƙashin jagorancin Saleh Zazzaga ce ta kai ƙarar Ganduje da APC da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Ƙungiyar ta ce naɗa Ganduje ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu wanda ya fito daga jihar Nasarawa a shiyyar Arewa ta tsakiya ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Don haka ne suke neman kotu ta soke duk wani mataki da Ganduje ya ɗauka a matsayin shugaban jam’iyyar APC tun bayan naɗa shi a ranar 3 ga Agusta, 2023.
A zaman koyun na yau Alhamis, lauyan wanda ya shigar da ƙara, Ayuba Abdul, ya lura da kasancewar lauyan Ganduje a kotu ba tare da tsammani ba duk da yunƙurin kai wa Ganduje takardar sammacin kotu ya ci tura.
DUBA NAN: Kotu Ta Hana Ganduje Bayyana Kansa A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC
Mai shari’a Ekwo ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yuni domin sauraren ƙarar da kuma ƙorafin farko, inda ya bayar da umarnin a bayar da sanarwar sauraren ƙarar ga INEC, wadda ba ta samu wakilci a kotun ba.