Kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da zaben gwamna Biodun Oyebanji na Jihar Ekiti da mataimakiyarsa Misis Monisade Afuye.
Kotun da ta yanke hukunci ranar Alhamis a Ado -Ekiti ta yi watsi da karar dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Mista Segun Oni.
A hukuncin da alkalin kotun, Mai Shari’a Wilfred Kpochi da mamba a kwamitin, Mai Shari’a Sa’ad Zadawa suka karanta, sun warware duk wasu batutuwan da suka shafi Oni da jam’iyyarsa ta SDP.
Kwamitin ya ce karar da Oni ya shigar kan Oyebanji da Afuye, “ya gaza samar da cikakkiyar hujja.”
A wani labarin na daban fusatattun gwamnonin jam’iyyar PDP guda biyar (G-5) sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
An ce dan takarar na jam’iyyar APC ya nemi amincewar gwamnonin biyar din da su mara masa baya a yayin wani gangamin taro da aka gudanar a ranar Talata.
Gwamna Nyesom Wike (Rivers), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue) da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da wasu jiga-jigan siyasa daga Kudu sun sha alwashin ba za su goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ba, sabida kin amincewa da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus bayan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai jam’iyyar PDP ta yi barazanar hukunta gwamnonin kan duk wani aiki da zai saba wa dokokin jam’iyyar, inda ta jaddada cewa tana da karfin ladabtar da duk wani gwamna da ya bijirewa dokar Jam’iyyar.