Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF ta fara nazari kan daukar sabon mai horaswar da zai jagoranci tawagar ‘yan wasan kasar, biyo bayan murabus din da kocin ‘yan wasan na Super Eagles Austine Eguavoen yayi.
A zagayen farko na karawar da suka yi an tashi babu ci 0-0 a Ghana, yayin da kuma a Najeriya aka tashi 1-1, abinda ya baiwa ‘yan wasan na Black Stars damar zuwa gasar cin kofin duniya ta bana.
Gabanin fara gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirka ne dai hukumar kwallon Najeriya ta sanar da korar tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr, inda ta nada Austine Eguaveon a matsayin kocin rikon kwarya, inda kuma aka sa ran bayan kammala gasar ta AFCON mai yiwuwa a sanar da Jose Pasiero tsohon kocin kungiyar FC Porto da ke kasar Portugal a matsayin kocin dindindin na kwallon Najeriya.
Sai dai kash, al’amura basu tafi kamar yadda aka tsara ba, kasancewar Najeriya. ta fice daga gasar cin kofin ta Afirka tun a zagaye na biyu, bayan rashin nasara a hannun Tunisia da 1-0.
Shi kuwa Pasiero da akai ta sa ran shi ne zai zama kocin dindindin, daga bisani hukumar NFF ta bayyana cewar babu wata yarjejeniya da aka cimma tsakaninsu da jami’in, wanda ya gaza bayyana a Kamaru domin sa idanu kan yadda wasannin Najeriya za su kaya a matsayin dan kallo, kafin ya soma jagorantarsu.