Mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya ziyarci Edo wurin ralin NNPP na kudu maso kudu.
Tsohon gwamnan ya bayyana banbancinsa da sauran yan takarar shugaban kasa da zasu gwabza a zabe mai zuwa.
Kwankwaso ya ce ya kai ziyara kananan hukumomi 500 cikin 774 da ake da su a Najeriya ba kamar sauran ‘yan takara ba.
Da yammacin Alhamis ɗin nan mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya dira Benin City, babban birnin jihar Edo.
Rahoton Vanguard ya tattaro cewa Kwankwaso ya ziyarci jihar ne domin halartar Ralin kamfen jam’iyyar NNPP na shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi ikirarin cewa shi ne ɗan takarar shugaɓan ƙasa ɗaya tilo da ya shirya jan ragamar talakawa saboda shi kaɗai ne ya ziyarci kananan hukumomi 500 cikin 774.
Ya bayyana cewa ya ziyarci inda tushen ‘yan Najeriya su ke yayin da sauran abokin gwabzawarsa suka maida hankali kan birane kaɗai.
Kwankwaso ya ziyarci anguwannin da ‘yan arewa suka fi rinjaye a birnin Benin wanda ya haɗa da Aduwawa, Layin Legas da sauran makamantansu.
Bayan nan ne ayarin tsohon gwamnan ya zarce zuwa Baptist Convention, wurin da aka shirya domin gangamin kamfen shugaban kasa na NNPP.
Yayin ralin, Kwankwaso ya miƙa tutar NNPP ga ‘yan takarar gwamna da ‘yan takarar Sanatoci daga jihohin kudu maso kudu, sannan ya roki mutane su zaɓi NNPP sak.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan Ralin, ɗaya daga cikin jagororin NNPP kuma ɗan takarar Sanatan Edo ta tsakiya, Okoduwa Akhigbe, ya ce: “Ɗan takararmu ya sa kafa ya ziyarci kananan hukumomi sama da 500 daga cikin 774 da muke da su a Najeriya, daga hirarasa da su ya gano cewa mafi yawan mutane ba su jin daɗin abinda ke faruwa.”
Shin NNPP zata iya kai labari a zaɓe?
Da yake tsokaci kan damar jam’iyyar ta samun nasara a zaɓe mai zuwa, Jigon ya ce: “Wa zai zabi APC? Kowa ya san jam’iyar ta gaza kuma ku tuna mutane sun kori PDP ne saboda ba ta yin abinda ya dace.
Shin kuna son komawa ga APC mafi munin jam’iyyar da ta gaza yin abu mai kyau?”
A wani labarin kuma Shugaban Kasa Buhari ya bayyana muhimman dalilai uku da suka sa ya shiga yakin neman zaɓen Tinubu Buhari ya faɗi haka ne yayin da suka kaiwa mai martaba Sarkin Musulmi ziyara a fadarsa dake birnin Sakkwato ranar Alhamis Shugaban kasan tare da Tinubu da sauran ‘yan tawagar kamfen APC sun je fadar ne gabanin zuwa wurin ralin da aka shirya a jihar dake arewa maso yamma.
Source:LegitHausa