Mako biyu gabanin zaben shugaban kasa, jam’iyyar APC mai mulki ta rasa dandazon mambobi a jihar Ebonyi.
Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, wanda ya karbi mutanen zuwa inuwar Laima ya ce lokacin da zasu kwace mulki ya yi.
Masu sauya shekar sun ce sun yanke shiga PDP ne saboda ba da gudummuwa a ceto Najeriya.
Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi ta karbi ɗaruruwan masu sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki ranar Jumu’a.
Rahoton Punch ya nuna cewa ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Dakta Ifeanyi Chukwuma Odii, wanda ya yi maraba da mutanen ya ce PDP ta shirya tsaf domin lashe zaɓe mai zuwa.
Ya ce: “PDP ta kawo sauyi mai kyau a jihar Ebonyi kafin a kwace mulki daga hannunta amma yanzu muna kokarin dawo da martabarmu.
Ina tabbatar wa mutanenmu da ikon Allah zamu cika manufofinmu.”
“Idan muka ci nasara zamu tabbatar kowane haifaffen jihar nan ya samu ilimi, zamu azurta mutane, ƙuncin rayuwa zai ƙare kuma matasa zasu samu ayyukan yi.”
“Wannan ya nuna PDP iyali ɗaya ne kuma zamu kara haɗa kai don samun nasara, jam’iyyarmu ta yi imani da zaman lafiya kuma tana fatan zaɓe ya gudana lami lafiya.”
“Muna muku maraba zuwa inuwar laima, inda kuka shigo yau kuma muna da wurin ɗaukar kowane mutum a Ebonyi da Najeriya baki ɗaya, ” inji shi.
Daga nan sai ya yi kira ga mazauna jihar da su dangwalawa jam’iyyar PDP tun daga sama har zuwa ƙasa, kamar yadda Rahoton Newsguru ya tabbatar.
Meyasa yan siyasan suka sauya sheka?
Emenike Jeff, wanda ya jagoranci masu sauya shekar daga gundumar Ugwuagu-Ndieto ta 2 a ƙaramar hukumar Izzi, ya ce sun zaɓi shiga PDP ne domin goyon bayan ɗan takarar da suka hangi yana da ɗabi’a mai kyau.
Mista Jeff ya ce: “Lokacin da nake cikin APC akwai abubuwa da dama da na gani gurɓatattu kuma a matsayin mai son zaman lafiya, ya zama wajibi na gudu zuwa PDP.”
“Na yi amanna da zaman lafiya kuma zamu haɗa karfi da karfe mu kawo wa jam’iyyar PDP yankin mu da baki ɗaya karamar hukumar mu.”
A wani labarin kuma Jami’Iyyar PDP Ya Zabi Sabuwar Ranar Zaben Fidda Dan Takarar Gwamna a Jihohi Uku Akwai jihohi Takwas a Najeriya waɗanda INEC ke gudanar da zaben gwamna a lokuta daban da lokacin babban zaɓen game gari.
Daga cikin waɗannan jihohi akwai Imo, Kogi da Bayelsa, kuma hukumar zabe ta shirya zabukansu a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Source:LegitHausa