Ministan kwadago Chris Ngige yayi gargadin cewa a zaben shekarar 2023 duk jam’iyyar data tsayar da dan takara daga Arewa ba zata ci zabeba.
Ya bayyana hakane a hirar da yayi da jaridar Vanguard.
Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma kara da cewa jihohin Inyamurai ne ya kamata su samar da shugaban kasa a shekarar 2023.
Hakanan yace tsarin karba-karba duk da yake baya cikin kundin tsarin mulki amma ya kamata a mutuntashi.