Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba ya yi alkawarin ba zai nuna wariyya a gwamnatinsa ba.
Tsohon sanatan na Kogi ta yamma ya kuma yi alkawarin cewa idan an zabe shi gwamna, zai yi mulki ne tare da ‘tsoron Allah’.
Malaye ya yi nasarar zama dan takarar gwamnan PDP ne bayan yin nasara a zaben fidda gwani da aka yi a ranar 16 ga watan Afrilu
Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a Kogi, ya ce zai yi gwamnati mai tafiya da kowa-da-kowa idan an zabe shi.
A cikin sanarwar da tawagar watsa labaransa ta fitar a ranar Asabar, dan takarar na PDP ya yi magana ne yayin ziyarar da ya kai fadar Abdulrazak Isa Koto, Ohimege Igu na Koton Karfi.
Melaye ya kara da cewa zai zama ‘gwamna na kowa” ba tare da la’akari da kabila ba.
A ranar 16 ga watan Afrilu, Melaye ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan Kogi a PDP, inda ya kada Idoko Ilonah, babban abokin karawarsa da kuri’u 189.
Zai fafata da Ahmed Ododo, na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben gwamnan da aka shirya yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Sanata Dino Melaye ba yana cigaba da rayuwarsa da ya saba na nuna wa duniya falalar da ubangiji ya masa na samun yalwa da rayuwa.
A wani bidiyo da ya fitar, Melaye ya nuna wa duniya wani katafaren gida da ya gina a kauyensu na Aiyetoro, Gbede, jihar Kogi a matsayin masaukinsa.
Source:LegitHausang