Mayakan ISWAP a Najeriya sun kashe akalla mutane 30 a kauyen dikwa a matsayin ramakon kashe kwamandan su da sojoji suka yi ta hanyar kai harin sama a Jihar Borno.
Majiyoyi daga yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mayakan sun kai hari ne a kauyen Mudu dake Yankin Dikwa a karshen mako.
Wani shugaban ‘Yan Sakai da ake kira Babakura Kolo a Maiduguri ya bayyana cewar mayakan sun yanka akasarin mutanen da suka kama ne wadanda maza ne dake kokarin tserewa daga yankin.
Kolo yace akasarin wadanda aka kashe ’yan gwangwan ne dake neman karafa daga motocin da aka kona ko aka daina amfani da su a yankin saboda hare haren mayakan book haram bayan sun je kauyen daga Rann wanda ke da nisar kilomita 80 a tsakanin su.
Wani shugaban ‘Yan Sa Kan Umar Ari yace mayakan ISWAP sun zargin wadanda suka kashen ne da baiwa jami’an tsaro bayanai game da harkokin su.
Rikicin boko haram yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 40,000 da kuma raba mutane sama da miliyan biyu daga muhallin su tun daga shekarar 2009.
A wani labarin na daban kuma wasu ‘yan sama jannatin kasar China uku sun koma doron kasa a wannan Asabar bayan shafe kwanaki 183 a sararin samaniya, lamarin da ya kawo karshen kumbo mafi dadewa a kokarin China na zama jagaba a harkar sararin samaniya.
Maza biyu da mace daya — Zhai Zhigang da Ye Guangfu da kuma Wang Yaping — sun dawo duniya ne da misalin karfe 10 na safe agogon Beijing, bayan da suka shafe watanni shida suna cikin jirgin Tianhe na tashar sararin samaniyar Tiangong na kasar China.