Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a karamar hukumar, Halliru Gwanzo ne, ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Gwanzo, ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne, sakamakon zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ke masa kan cin hanci da rashawa.
Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aikin ne daga yau Litinin 15 ga watan Afrilu, 2024.
A wani labarin na daban jarumin masana’antar Kannywood Adam A Zango a wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, ya bayyana cewar babu wani abin ke damun kwakwalwarsa.
Tunda farko dai an ga jarumin wanda wasu ke kallo da mutum mai auri saki ya yi wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda yake bayyana wasu abubuwa marasa dadi dake faruwa a tsakaninsa da iyalinsa.
“Na kama matata da laifin yin dan malele amma na ci gaba da zaman aure da ita.
“An tura min bidiyon batsa da matata ta yi da kanta akan na biya Naira milyan daya ko a saka a duniya na yi hakuri na ci gaba da zaman aure da ita.
“Na kama matata da cin amanata da dan uwana na yi hakuri na ci gaba da zaman aure da ita.
“Idan na yi musu kazafi Allah Ya tona min asiri tun a duniya.
“Ku fada min maza nawa ne masu imanin da za su iya hakuri kamar yadda na yi?
“Idan kuna bukatar shaidu ku rubuta min witness a comment section”.
DUBA NAN: Gwamnan Kano Ya Bukaci EFCC Ta Cigaba Da Binciken Dala
Hakan ya sa wasu suke ganin jarumin ba ya ciki hayyacinsa a lokacin da yake wadannan jawabai saboda ana ganin cewa abu ne da ya kamata ya sirrinta ganin cewa abu ne wanda ba kowa ya kamata ya sani ba.