Sanata Aisha Binani, yar takarar gwamnan APC a jihar Adamawa ta samu kyakkyawar tarba daga dandazon masoyan ta a garin Yola.
Magoya bayan Binani sun taru don yiwa yar takarar murnar dawowa mahaifarta karo na farko tun bayan da tayi nasara kan Nuhu Ribadu.
Kotun daukaka kara ce ta dawo da sanatar kan kujerarta a matsayin sahihiyar yar takarar gwamna a zaben fidda gwanin jam’iyya mai mulki.
Dandazon magoya baya sun yi turuwa don yiwa Sanata Aishatu Ahmed Binani maraba da dawowa karo na farko bayan kotun daukaka kara ta dawo da ita a matsayin yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
Binami wacce ta dawo Yola a karshen mako ta samu kyakkyawar tarba tun daga filin jirgin sama na Yola har zuwa manyan unguwanni da ke sada mutum da sakatariyar APC da ke hanyar Bank Road, karamar hukumar Yola ta arewa.
Bayan Nasara Da Ta Samu Kan Ribadu, Dandazon Jama’a Sun Tarbi Aisha Binani a Jihar Adamawa Hoto: Daily Trust
Hakazalika magoya baya sun mamaye hanyar Jimeta-Yola har zuwa gidanta da ke garin Yola a karamar hukumar Yola ta Kudu, wasu a kafa wasu a motoci suna saka wakokin yabon Binani, jaridar The Nation ta rahoto.
Tun a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba ne jihar Adamawa ta dauki harami bayan kotun koli ta ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben fidda gwanin gwamnan APC da aka yi a watan Mayu.
Binani ta nemi su hada kai da Nuhu Ribadu da sauran ‘yan jam’iyya
Binani, wacce bata nan a lokacin da kotun kolin ta zartar da hukunci, ta dawo Yola a yammacin ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba inda ta tarar da dandazon magoya bayanta da suka hada da manya da kanan ‘ya’yan APC da sauransu.
A sakatariyar APC na jihar, Binani ta bayyana cewa nasararta na jam’iyyar ne sannan ta bukaci a hada kai inda ta nemi babban abokin hamayyarta, Nuhu Ribadu ya zo su hada hannu a wannan tafiya.
Ta ce:
“Ina bukatarmu mu dukka da mu binne banbancinmu sannan mu hade a matsayin tsintsiya daya don tabbatar da nasarar yan takarar APC a 2023.
Mu fahimci tunshen banbance-banbancenmu sannan mu magancesu a matsayin harkokin cikin gida na jam’iyyarmu.
Ba za mu iya cimma nasara da rababben gida ba. Karfinmu na cikin hadin kanmu.”
Ma’ajin jam’iyyar NNPP ya sauya sheka, Bashir Ahmad ya yi murna.
A wani labarin kuma, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad na zawarci ma’ajin jam’iyyar NNPP, Shehu Ningi wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Ahmad ya ce suna fatan yiwa Ningi maraba da zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC gabannin babban zaben 2023.
Source:Legithausa