Dan takarar gwamna, Sa’idu Gumburawa, ne ya jagoranci yan takarar majalisun tarayya na majalisar dokokin jiha zuwa APC.
Baki ɗaya ‘yan takarar jam’iyyar PRP a jihar Sokoto sun aje tikitin su, sun koma jam’iyyar APC a jihar Sokoto.
Sanata Aliyu Wamakko, wanda ya tarbi masu sauya sheƙar hannu biyu karkashin jagorancin dan takarar gwamnan, yace wannan ba ƙaramar nasara bace.
‘Yan takarar kujeru daban-daban na jam’iyyar PRP a jihar Sakkwato karkashin jagorancin ɗan takarar gwamna a 2023, Sa’idu Gumburawa, sun sauya sheƙa zuwa APC.
A cewar hukumar labarai ta ƙasa (NAN), hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wamakko, ya fitar.
“Mun yi nazari kan halin da Sakkwatawa suka shiga karkashin mulkin PDP kuma hakan ya ƙara man kwarin guiwar shiga APC domin taimaka wa jiharmu ta dawo kan turbar nasara da take a mulkin Wamakko.”
Bayan Gumburawa, sauran waɗanda suka bi sawunsa zuwa APC sun hada da ‘yan takarar Sanata na shiyyoyi uku a inuwar PRP, Garzali Abdullahi, Bello Holai da Shehu Ibrahim.
“Haka nan kuma ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya 11 da masu neman shiga zauren majalisar dokokin jihar Sokoto 30 na cikin waɗanda suka koma APC,” inji Abubakar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Wannan babbar nasara ce a APC – Wamakko Sanarwan ta ƙara da cewa ‘yan takarar jam’iyar PRP a 2023 sun samu tarba hannu bibbiyu daga jagoran jam’iyyar APC a Sakkwato, Sanata Wamakko.
Da yake jawabi kan cigaban, Wamakko yace wannan sauya sheƙar na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da APC ta samu a jihar gabanin babban zaɓen 2023.
“Na ji daɗi abokina kuma abokin kokarin kawo cigaba, Gomburawa, ya dawo gida ya haɗa hanu damu a kokarinmu na gina cigaba mai ɗorewa a Sokoto.”
“A yau ina tabbatar maka da cewa APC da kafatanin mambobinta zasu yi aiki da kai da sauran ‘yan tawagarka domin cika burin nasararmu a zabe mai zuwa.” – Aliyu Wamakko.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP sun yi gagarumin rashin ƙungiyoyin magoya baya 10 a arewa ta yamma Kungiyoyin, waɗanda ke tare da Atiku tun shekarar 2015 sun sauya sheka zuwa APC, sun cacci tsohon mataimakin shugaban ƙasa kan watsi da aikinsu.
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci a sanya mutanen cikin kwamitin yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima na shiyyar don su ba da gudummuwarsu.
Source:Legithausa