Wani dan kunar bakin wake ya kashe fitaccen dan jaridar kasar Somalia da ya shahara wajn caccakar kungiyar al-Shabab a yayin da yake fita daga wani gidan cin abinci a Mogadisahu, babban birnin kasar.
Harin ya raunata mutane da dama, ciki har da daraktan gidan talabijin Somalia da wani direba.
A wani labarin na daban mai kama da wannan a wata sanarwa, mataimakin ministan yada labaran Somalia, Abdirahman Yusuf Omar ya ce kasar ta yi asarar jajirtaccen namiji kuma dan kasar
Abdiaziz ya yi fice ne saboda wani shirinsa da yake ganawa da ‘yan kungiyar al-Shabab da jami’an tsaron Somalia ke tsare da su, shirin da ya samu dimbim mabiya a ciki da wajen kasar.
Hukumomin Somalia sun harbe wani malamin makaranta tare da wasu mutane biyu a bainar jama’a saboda samun su da laifin kisa a madadin kungiyar Al Shebaab.
Malamin Mohammed Haji Ahmed da ke koyar da Turanci a kwalejin Mogadishu na da hannu wajen kashe jami’an gwamnati da dama a madadin kungiyar Al Shebaab.
Rahotanni sun bayyana shi a matsayin mara Imani, wanda ya yi kaurin suna wajen aikata kisan ciki harda na Janar Abdullahi Mohammed Sheikh a shekarar 2017 da mataimakin babban lauyan gwamnati Mohammed Abdurrahman Mohammed a shekarar 2019 da kuma shugaban ‘yan Sanda janar Mohammed Haji Alow.