Babban dan Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Abdulazeez Ganduje, ya yi barazanar kai mahaifinsa kotu in har ba’a biya shi cikon kudin da yake bi na kwangila ba.
A ranar 7 ga Mayu 2021 ne dai Ganduje ya bawa kamfanin Abdulazeez mai suna Global Firm Limited kwangila ta naira miliyan 189 kuma aka biya shi naira miliyan 82 bayan ya fara aikin.
Amma sai dai gwamnan daga bisani ya ki biyansa cikon kudin duk da ya gama aikin.
Wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa rashin biyan nasa cikon kudin na da alaka da kai karar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat Ganduje da ya yi ga hukumar EFCC a shekarar da ta gabata.
A zantawar da jaridar DAILY NIGERIAN ta yi da Abdulazeez, ya tabbatar da cewa ya yi duk iya kokarin da zai yi kudinsa su fito amma sun ki fitowa.
Ya kuma shaidawa wakilinmu cewa rashin biyan nasa na da alaka da takardar da ya kai EFCC, kana kuma da turjiya da ya yi wajen kin bada na-goro ga Gidauniyar Ganduje (Ganduje Foundation).
A takardar da ya rubutawa maaikatar Ilimi ta Jihar Kano ta hannun lauyansa Barista Umar Shehu, Abdulaziz ya ce idan ba’a biya shi kudin nan cikin kwana bakwai ba, to kuwa zai dauki matakin sharia.