Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi.
Bisa dalilin cewa sunan Peter Obi ta kama bakunan yan Najeriya, amma Patrick Obahiagbon baya tunanin zai iya cin zaben shugaban kasa na 2023.
A cewar tsohon dan majalisar, dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party ba zai iya cin kashi 25 cikin 100 na kuri’u a jihohi 24 ba.
Obahiagbon ya bayyana magoya bayan Peter Obi a matsayin yan Najeriya da suka gaji da yan siyasa na yanzu kuma suke son wani sabon abu.
Jigon na jam’iyyar APC ya ce matasan Najeriya sun fara nuna rashin gamsuwarsa da abubuwan da ke faruwa a kasar ne a zanga-zangar EndSARS.
Patrick Obahiagbon, tsohon dan majalisa na wakilai na tarayya, ya ce ya yi imanin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, ba zai iya cin zaben shugaban kasa na 2023 ba.
Tsohon dan majalisar yayin hirar da aka yi da shi a shirin The Morning Show a Arise Television ya ce jam’iyyun APC da PDP ne manyan jam’iyyun da za su fafata a zabe.
Amma, jigon na APC ya bayyana cewa duk da cewa manyan jam’iyyun siyasa biyu na kasar ne za su fafata a zaben, akwai manyan takarar shugabn kasa uku, suna Bola Tinubu (APC), Atiku Abubakar (PDP) da Peter Obi (LP).
Obahiagbon ya ce: “Ban ga yadda za a yi Labour Party za ta iya samun kashi 25 cikin 100 a jihohi 24 a wannan zaben ba.”
Su wanene magoya bayan Peter Obi?
Obahiagbon ya ce wadanda ke goyon bayan takarar shugabancin kasa na Obi yan Najeriya ne da suka gaji da yan siyasa na zuwa, The Cable ta rahoto.
Ya bayyana tafiyar ta ‘Obidient’ a matsayin ‘sabuwar tafiya.
Tsohon dan majalisar ya ce tafiyar ta Peter Obi na da alaka da rashin gamsuwar da matasa suka yi da abubuwa a kasar kamar yadda suka nuna yayin zanga-zangar ENDSARS a 2020.
Ya yi tambaya: “Shin Peter Obi zai iya amfani da fushin da yan Najeriya suka yi ta yan siyasan yanzu ya shiga Aso Rock?
Ina ganin ba zai yi wu ba.
Bana ganin hakan zai yi wu.” Obahiagbon ya ce yana fatan yan siyasan Najeriya za su koyi darasi daga abin da ya janyo matasa suke goyon Peter Obi.
Source; LEGITHAUSA