A farkon wannan makon ne wasu da suka yi ikirarin cewa su ne shugabannin mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa suka sanar da dakatar da shi daga matsayin mamba na jam’iyyar a matakin mazaɓar.
A umarnin da kotun ta bayar ranar Laraba, ta umarci uwar jam’iyyar ta ƙasa da kuma Abdullahi Umar Ganduje su tsaya a matsayinsu tun daga ranar 15 ga watan Afrilu
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa.
A farkon wannan makon ne wasu da suka yi ikirarin cewa su ne shugabannin mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ne suka sanar da dakatar da shi daga matsayin mamba na jam’iyyar a matakin mazaɓar.
Mai magana da yawun kotunan Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim wanda ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa labarin, ya ce an ɗauki matakin ne bisa wata ƙara da wasu mutum biyu suka shigar a kan APC da Shugabanninta na ƙasa da na jihar Kano da kuma shugabanta na ƙasa Abdullahi Ganduje.
“Haladu Gwando da Laminu Sani Barguma sun nemi abubuwa da dama a kan ƙarar da suke yi ta waɗannan mutane, daga ciki kotu ta sahhale musu wasu abubuwa ciki har da sadar da sammacin ga wadanda ake ƙara a Abuja, saboda ya ƙetare iyakar hurumin da kotun take da shi na yin hakan da kanta.
Umarnin Kotun Kano a kan Ganduje
“Na biyu kuma sai aka ba da umarnin wucin-gadi cewar an umarci jam’iyyar APC cewa su tsaya a inda suke tun daga ranar 15 ga watan Afrilu kan abin da ya shafi dakatar da shugaban Apc na ƙasa da aka yi,” a cewar Baba Jibo.
Mai magana da yawun kotunan ya ce abu na gaba shi ne za a koma sauraran ƙarar ranar 30 ga watan Afrilu.
Mafarin zance
Za a iya cewa wannan lamari na ikirarin da wasu da suka ce su shugabannin jam’iyyar APC ne na mazabar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano na dakatar da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya zama wata sabuwar dambarwar siyasa da ta kunno kai a jam’iyyar APC a Kanon.
Shugabannin sun ce sun dauki matakin dakatar da tsohon gwamnan jihar ne saboda zargin da gwamnatin jihar Kano ke yi masa na cin-hanci da rashawa.
Wata dambarwar siyasa ta kunno kai a jam’iyyar APC ta Jihar Kano bayan da wasu da suka yi ikirarin cewa su shugabannin jam’iyyar ne na mazabar Ganduje suka dakatar da shugaban APC na ƙasa Abdullahi Ganduje
Ga nazari kan abin da dambarwar da abin da take nufi a siyasance.
A daya bangaren, jim kadan bayan sanarwar dakatar da aka yi wa Ganduje a mazabarsa, sai Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano Abdullahi Abbas ya sanar da dakatar da shugabannin jam’iyyar mazabar Gandujen har tsawon watanni shida kan zargin suna yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Sannan shugaban jam’iyyar na jiha ya ce dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamna Ganduje ba ta halasta ba.
Ya ce wadanda suka dauki matakin ba ’yan APC ba ne kuma jam’iyyar za ta gurfanar da su a gaban kuliya.
Kazalika shugaban jam’iyyar ya ce suna da hujjoji kan ganawar da wasu jami’an gwamnatin jihar Kano suka yi da wadanda suka ce su ne shugabannin mazabar Ganduje da suka dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Ko a ranar Laraba a wani bidiyo, an ga shugaban jam’iyyar APCn Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa ba, yana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ne ya tabbatar masa cewa “kujerar nan tana nan daram.”
Shugaban jam’iyyar APC a Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa ba, yana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ne ya tabbatar masa cewa “kujerar nan tana nan daram.”
Sai dai Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa ba su da hannu a dambarwar da take tsakanin Ganduje da shugabannin mazabarsa, inda yace matsalarsu ce ta cikin gida.
Ana cikin haka ne kuma sai aka ba da rahoton cewa shugabannin mazabar ta Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a Kano sun kai wa shugaban na APC na Abdullahi Umar Ganduja ziyarar jaddada goyon bayan a babban ofishin jam’iyyar a Abuja.
Idan ba a manta ba a watan Janairu da ya wuce ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya shawarci Ganduje ya yi sulhi da bangaren Kwankwasiyya. Hakan ne ya sa a wata ziyara da ya kai Kano, ya gayyaci Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya shiga cikin jam’iyyar.
Idan ba a manta ba a watan Janairu da ya wuce ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya shawarci Ganduje ya yi sulhi da bangaren Kwankwasiyya.
Hakan ne ya sa a wata ziyara da ya kai Kano, ya gayyaci Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya shiga cikin jam’iyyar.
DUBA NAN: APC Ta Kori Ganduje Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Wanda wasu masana suka kalla a matsayin shirye-shiryen tunkarar zaben shekarar 2027 ne.